Sakon maraba daga marubucin shafin Bahaushen Arewa.
Assalamu Alaikum 'yan uwa Hausawa.
Wannan shine karo na farko da nake son fara tura sakonnina zuwa gareku domin nuna kauna da kuma kyautata alaka ta tsakanina da ku a matsayina na Bahaushe mazaunin Arewa.
Na zauna nayi nazarin ganin wace hanya zan bi domin bada tawa gudunmuwa a wannan zamani da muke ciki, bayan 'yan shawarwari da na samu da kuma bincike-bincike da suka gudana, sai na yanke shawarar bude wannan shafi na Bahaushe.
Wannan shafi nawa na Bahaushen Arewa zai mayar da hankali ne a kan labaru wanda suka kunshi namu na gida, ina nufin na Arewa da kuma ma wanda suka shafi kasar mu Nigeria baki daya. Sannan kuma wannan shafi zai mayar da hankalinsa ne ga siyasar mu ta arewa da kuma ta kasa baki daya duba ga yanda matasan Arewa suka fara mayar da hankalin su kan siyasa.
Zan dinga kawo maku labaru da dumi-dumin su ku karanta a cikin nutsuwa ba tare da ka jira wani ya baka labari ba, sai kuma dan nazari da bincike da nayi wanda ya shafi matasan mu domin kawo muna cigaba. Sannan shafin zai dinga watsa manufofinsa ne ta yaren harshen Hausa kamar yanda kuke gani a sakon maraba da kuke karantawa yanzu.
Ina mika gaisuwata ga dukkan wani Bahaushe da yake zaune a gida Arewa ko a waje. Ina fata wannan manufa tawa ta kasance hanyar hada kyakyawar alaka ta a tsakanina da ku.
Sannan daga karshe ina mai fata Allah Ubangiji ya bani sa'a domin gudanar da harkoki na cikin sauki da kuma nasara, Allah ya kare ni daga aikata barna.
Allah ya kawo muna saukin rayuwar da muka tsinci kan mu a wannan kasa tamu ta haihuwa. Allah ya yaye muna dukkanin bakin ciki da kuma asara a duniya da kiyama.


0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home