Thursday, 19 October 2017

Kungiyoyin Matasa.

Matasa! Shin ko kun san kuna da muhimmiyar rawa wadda zaku iya takawa a yankunanku?

Duba da yanda halinda ilimi yake a ciki a kasar mu musamman nan gida Arewa, yasa nayi wannan rubutu domin fadakarwa ga matasan mu da tunatar da su muhimmacin ilimi da kuma rawar da zasu iya takawa wajen karfafawa na kasa dasu dan cigaban mu.

Ilimantarwa da tarbiyya al’amura ne masu girman matsayi da daukaka kuma sune ginshikin rayuwa da suke kai mutum ga kyakkyawar rayuwa da samun cikan kamala. Hakika mutum wani halitta ne da ke bukatar tarbiyya a fagen rayuwarsa kuma sakamakon kyakkyawar tarbiyya  zai iya kai wa ga babban matsayi na tsarkakan ruhi da yalwan ilimi a rayuwarsa ta duniya. Hakika tun daga yarantar mutum har zuwa girmansa da kuma zuwa karshen rayuwarsa yana rayuwa ce a kan matakai masu bibiyar juna kuma a tsawon matakan rayuwarsa yana da damar kai wa ga mataki madaukaki, kamala da cika.

Hakika matakin kula da tarbiyyar yara lamari ne mai muhimmanci da ke bukatar sanya ido da lura, kuma dole ne a kan mahaifa ko masu kula da tarbiyyar yara su kasance masu cikakken sa- ido kan tarbiyyar yaran da lura da dabi’unsu. A fili yake cewa tarbiyya da ilimantarwa al’amura ne masu muhimmanci da daukaka a rayuwar mutum musamman daga lokacin yaranta zuwa lokacin samartaka, kuma wadannan matakai biyu na yaranta da samartaka suna kunshe da tarin matsaloli na musamman, sakamakon haka tarbiyya da ilimantarwa suna da matakai, kuma kowane mataki yana da nashi matsayi da muhimmanci na musamman.
Tarbiyya a ma’anarta ta lugga tana nufin karuwa, girma da habaka a kan tafarkin da ake bukata, ko kan tafarki mai kima. Yayin da neman ilimi hanya ce da take kai mutum ga samun tarbiyya da kyakkyawan sakamakon rayuwa. Don haka a fili yake cewa neman ilimi da samun tarbiyya sune shimfida kuma ginshikai da suke kai ga inganta rayuwar bil-Adama tare da taimaka masa wajen cimma burin rayuwarsa na kai wa ga matsayin cika da kamala da ake bukata.

Akwai kungiyoyi da dama masu zaman kansu wato 'Non Governmental Organisations' NGO a takaice wanda suke a nan gida Arewa sunyi niyyar taimakawa wajen bada kula ga harkokin karatu  musamman na yara kanana da kuma marayu marasa galihu, shin ko ka shirya taimakon alu'ummmar ka? Ta wace hanya zaka iya bada gudunmuwarka domin cigaban Arewa? Wannan sune tambayoyi wanda ya kamata kayiwa kanka su.
Wata kungiyar matasa da naci karo da su ne yasa nayi wannan 'yar tunatarwar ga matasan mu na Arewa domin ganin yanda suka shirya tsaf dan tallafawa yaran Jahar Zamfara wurin karatun su.
A kasa zaka iya ganin su a cikin hoto. Ko da gani, ba sai an gaya maka ba lallai sun shirya tsaf dan ganin cewa yaran jahar su sun samu tallafi daga garesu. Shin ko kaima kana da niyyar taimakawa dan ganin an karfafawa ilimi a Arewa?

Wannan kungiyar matasan da na hadu da su a wata makaranta mai suna Ibrahim Gusau sun yiwa kansu suna da Juvenile Aid Foundation.

Wasu daga cikin Matasa 'yan kungiyar Juvenile Aid Foundation


Hakika wadannan matasa abun koyi ga sauran matasa da suke da karfi da kuma ikon tallafawa iyakar gwargwado domin ganin ilimi ya samu shiga a cikin dukkan wani kauye da ke Arewacin kasar nan.

A kasa zaku iya ganin yara 'yan makaranta da kuma sauran matsan nan na kungiyar Juvenile Aid Foundation.

Yara ;yan makaranta.
Idan ka duba daga kasa kuma, zaka ga shugaban Kungiyar yayin da yake mika kyauta ga wani dalibi.
Sugaban Kungiya yayin da yake mika kyauta ga wani dalibi.









Labels: ,

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home