Tuesday, 7 November 2017

Wayar Salula:Zuma ga Zaki ga Harbi




A wannan zamani da muke, idan ka duba a cikin al’ummar mu, waya ta zama ruwan dare a tsakanin kananan yara da matsan mu, ganin haka ne ma yasa marubucin yayi nazari game da irin illar da waya take yi ga matasa da kananan yara.
Ita Kalmar karamin yaro a kundin tsari tana nufin yaro ko yarinya wanda bai haura shekaru 18 ba (a takaice wanda bai balaga ba) dalili kuwa shine a bincike na masana sun yi amanna da cewa sai mutum ya kai shekara 18 ne ya soma mallakar hankalinsa, a wannan shekaru ne dokar kasa ta hau kan shi.
To a hakikanin gaskiya, duk abu wanda aka kirkira, yanada alfanu, haka zalika yana da illoli tari duk da cewa shi Alexander Graham Bell (wanda ya kirkiri wayar tarho) bai da makusa, yayi amfani da hikimarsa ne wurin bada tasa gudunmuwa dan cigaban dan Adam a rayuwa duk da cewa an samu wasu sauye-sauye bayan tashi fasahar. Ban sani ba ko akwai wata doka da ta hana matasa ‘yan kasa shekara da 18 amfani da wayar salula ba, saboda har yanzu akan bincike nake dan gani ko zan samu. Kididdiga ta nuna cewar kaso 78% a cikin 100% na yara dake tsakanin shekara 12-17 sun riga sun mallaki wayar salula. Amfani da wayar salula da matasa ‘yan kasa da shekara 18 ke yi ya zama barazana ba ma akan su kawai ba, a’a har ma ga al’umma duka.
A nan marubucin ya iyakance kansa ga illolin wayar salula a hannun matasa da kananan. Kafin mu tattauna illolin, ga wasu daga cikin amfaninta/muhaimancinta:
    

  •   Zumunci: Waya ta taimaka sosai wurin sada zumunci. Sada zumunci ta hanyar hada ‘yanuwa wanda suke nesa da juna.
  • Kasuwanci: Waya tana taimakawa wurin gudanar da harkokin kasuwanci. Manyan ‘yan kasuwa da ma kanana suna amfani da waya sosai domin gudanar da harkokin kasuwancin su, a yau mai son siyan kaya a wurin wani dan kasuwa zai iya daga wayarsa daga gida ya kira abokan cinikin sa dan siya ko siyar da hajarsa a nan  gida Najeriya ko a kasar waje.
  • Agajin gaugawa: Wayar salula ta taka muhimmiyar rawa wurin sadarda agaji na gaugawa. Misalin maras lafiya zai iya amfani da wayarsa dan kiran wani dan’uwan nasa ko kuma ya kira likita domin dauki a gareshi.
To wannan kadan kenan daga cikin alfanu na wayar salula, wanda zai iya kasancewa manya har matasan suna amfanuwa da shi. Amma illolin wayar salula gasu zan zayyano a kasa; 

Lalacewar tarbiyya: Saboda samun cigaba na zamani da ya auku, kamar yadda aka ambata a baya, wayar salula tayi jagora sosai da gaske wurin wargaza tarbiyyar matasa. Idan kayi duba ga yanar gizo gizo, akwai manhjoji da suke basu da aiki wanda ya wuce zuba hotuna da bidio na kallo wanda suke kunshe da batsa da nuna tsiraici. A bincike na masana da aka gudanar kwana-kwanan nan ya nuna cewar akwai irin wadannan manhajoji akan yanar gizo sama da dubu dari. Haka binciken ya nuna cewa, Najeriya tana daya daga cikin kasashe wanda sukafi kowa shiga wannan shafuffuka, wannan abun iyaye su duba ne, su saka ido akan ‘yan ‘yansu domin ganin sun kubutar da su daga irin shafuffukan, dalili kuwa shine kowa ya sani a addinnace walau Krista ko Musulmi cewa bayyanar da tsiraici bai karbuwa ga al’ummar mu domin yana taimakawa wurin rugejewar tarbiyya da samun barna ta bangaren fyade, haka ma yana ruguza al’umma da imaninsu. Akwai abunda ake kira da ‘cybersex’ a turance, ma’anarsa shine zina ta yanar gizo ko shafukan sada zumunta wanda hakan yana faruwa ba tare da sanin iyaye ba. Yana faruwa ta hanyar kiran waya ko kuma zance a shafukan sada zumunta. Masu wannan dabi’a suna bin hanyar taba al’aurar su dan su biyawa kansu bukata. Wannan ba karamin fasadi bane garesu da kuma al’umma baki daya.

Haduwa da abokai bata gari: A nan Kalmar aboki bata gari yana nufin aboki wanda yake neman wanda zasu yi tarayya da shi wurin wata harka ta barna. Daga gida ko a wani wuri, wani saurayi zai iya hada lambobi a wayarsa ya danna kira, burinsa ya samu mace ta daga wayar. Idan yayi nasa kuwa ya samu macen ta dauka sai ya gabatar da manufofinsa, idan itama ra’ayinta yayi daidai da nasa shikenan sai barna ta auku. Idan kuwa yayi rashin nasara aka samu akasin bata karbi ra’ayin nasa ba, sai yayi kokarin jawo hankalinta da kalamai har ta dawo ta amince da zancensa saboda karancin wayo.
    
     Tabarbarewar Karatu: Binciken masan ya nuna cewar yawan amfani da da wayar salula da matasa keyi yana haifar da koma baya ga iliminsu. Wannan ne ma yasa makarantu da dama suka hana dalibansu mu’amula da wayar salula yayinda suke cikin farfajiyar makaranta. Daliln haka kuwa abune mai saukin fahimta. A wannan zamani da muke ciki ya sanya bincike yayi karanci a tsakanin matasanmu ta hanyar yin amfani da shafin ‘Matambayi Baka Bata’ wato GOOGLE turance. Yana taimakawa wurin satar amsa matuka. Shi wannan shafin yasa matasanmu sun manta amfanin dakunan karatu wato ‘Library’. Sannan kuma ita wannan salular tana kunshe da na’urar lissafi da na’urar daukar hoto, duka wannan suna taimakawa wurin dauke hankali a lokacin darasi.
    
     Cãca: Shafuka da ake ta kirkirowa a yanzu dangin cãca sun zama ruwan dare. Misalin irin su akwai ‘9jabet, NairaBet, 365bet’ sun taimaka kwarai wurin afkawar matasanmu da yara kanana cikin halaka domin shafin yana bada dama da duk wanda ya shiga yayi zabi tsakanin kungiyoyin kwallon kafa wadda za tayi nasara akan wata ta hanyar sadaukar da wasu kudade.
  
     Rashin Isasshen Barci: Hakika barci yana da matukar amfani ga matashi. A kowacce rana matashi yana bukatar yayi barci na awa 9 da rabi to amma wasu basu amfani da wannan damar dan ganin sun cimma wanna awowin suna barcin sai dai su mayar da hankalinsu ga yanar gizo ko shafukan sada zumunta irin su Facebook ko Whatsapp. Zaka ga matashi ya kwashe lokaci mai tsawo yana rike da wayarsa, ya hana idanunsa runtsawa  a karshe sai kaga yaro idan yaje aji wurin darasi ka sameshi yana barci wannan illar ta jawo koma baya ta hanyar neman ilimi.

        Sirri: A wannan zamani da muke ciki yanzu, zamani ne wanda sirrin mu gaba daya bamu da tabbacin sa kuma yana kara kasancewa cikin barazan idan muka barshi a fili ta hanyar da makiya zasu iya amfani da shi wurin zambatarmu da wannan damar. Abun mamaki ne ga yanda wani bincike ya nuna cewar kashi 52 na matasa basu kashe na’urar GPS da ke a cikin salularsu idan suna amfani da yanar gizo ko shafukan sada zumunta. Wasu har sun kai matsayin da suna yada adireshin su a shafukan sada zumunta, daukar hotuna a gidajen su suna aikawa kai har ma hada lokaci na sirri dan saduwa ta fuska da wani wanda basu taba gani ba a zahiri sai dai fira a yanar gizo. Wannan bai tsaya nan ba, wasu sun kai matsayin suna bayyana zuri’arsu ko rayuwarsu wadda ta shafesu ga abokai da ko wani bako a shafukan sada zumunta.  Ni da kaina nayi badda kama nayi fira da wata karamar yarinya, abubuwanda ta fada mun game da rayuwarta ya gigita ni, har ta kai tana fada mun sirrikanta na boye. Wannan abu ne mai matukar tsoratarwa.


Iyaye sun bijiro da dalilai daban-daban  da yasa suke so ‘ya’yansu su mallaki wayar salula. Ya kamata ayi nazari mai zurfin gaske tsakanin amfaninta da kuma illolinta kafin a basu damar rika wannan na’ura. Wani mai bincike ya saki bidiyo na kallo inda ya nuna yanda yake magana da matasa a asirce ta shafukan sada zumunta kai har ma hada wata haduwa ta musamman a wani kebantaccen wuri. Yayi hakan ne tare da sanin iyayen su  dan ya nusar da su iyayen illar wayar salula. Zaka iya kaddara yanda karshen labarin ya kasance idan ace wani mutum ne wanda ba’a san asalin sa.

Balaga, kaifin tunani da kalar wayar dake hannun matasa da makamantansu, sune ya kamata a duba kafin a baiwa wani matashi damar rike waya. Haka zalika, tsauraran matakai na bukatuwa wurin kula da hanyoyi da yara suke mu’amula da waya. 
Kar ka manta ka danna maballin like dan nuna jijinawarka ga marubucin. Bugu da kari ma, zaka iya bata taka gudunmuwa ta hanyar yin comment dan nuna jin dadinka. Yin hakan zai kara kwarin guiwa ga marubucin.
© Muhammad Sunusi Nalado
+2347030339117
Sahfin Bahaushen Arewa
2017.

Labels: ,

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home