KO KUN SAN MUHIMMANCIN MATA KUWA?
ILIMI DA MUHIMMANCINSA GA MATA
Kafin zuwan wayewar kai da ilimi, mata basu da fada
aji cikin al’umma. An dauki mata ba a bakin komi ba face masu dawainiyar
gida da kula da ‘yara. A zamanin jahiliyyah a kasar Saudiya birne ‘ya’ya mata
akeyi da ransu, mata basu da gado, an dauke su kamar rigar da ake canzawa ko
wane lokaci aka ga dama.
Karatun ‘ya mace ba karamar fa’ida yake da shi
al’umma ba. Sabili da mahaifiya ita ke tare da yara kullum a gida, ilimin zai
sa kanta ya waye ta san muhimmancin karatu, zuwa asibiti, bawa yaranta
tarbiyyah ta kwarai ta inda har zasu zama masu kishin kasa. Mace me ilimi
zata taimaka wurin bawa mijinta shawarwari masu amfani da zasu taimaka wurin
gudanar da harkokin yau da kullum.
Har ila yau, yara mata dake karkara ana tauye musu
hakkin su na rashin samun ingantaccen ilimi ta hanyar aurar dasu tun a shekarun
da basu wuce kirgen dangi ba. Wala Allah in tasami miji me kishin karatu yasakata,
wala Allah kuma ta qare da jinyar yoyon fitsari bayan mijin ya mata sakin
wulakanci. Ba addinin da ya hana neman ilimi a duniya. Annabi Muhammad
tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace neman ilimi wajibi ne
akan kowane Musulmi, Tirmidhi ne ya ruwaito shi lamba ta saba’in da hudu.
Shawarar da zan bawa gwamnati shine, a saka
dokar dole sai yarinya ta kai shekaru sha shida kafin a aurar da ita. Akalla
kafin nan ta kara sanin ciwon kanta, ta gama karamin mataki na makarantar
gaba da firamari da kuma ilimin yin ginshiqan musulunci ba tare da ta kwafsa
ba. A kuma saka taran duk mahaifi koh marikin yarinyar da ya aurar da ita kafin
shekarun da aka kayyade koh ya hana ta zuwa makaranta ya biya kudi masu
yawan gaske koh zaman gidan maza na shekaru adadin kudin.
A lokutan baya, ba a baiwa ilimi muhimmanci ba kuma ba a damu a ba
‘ya mace ilimin addini ba ballantana na zamani. Har ana cewa “Sabbi saukar
Mata”. Watau da sun kai Suratul Sabbi shi ke nan sun bar karatu da neman ilimi.
Suratul Sabbi kuwa ita ce Surah ta 97 a Alkur ‘ani, kuma ita ce Izifi na daya
daga cikin Izifi Shittin na Alkur’ani.
Mace a wancan zamanin, idan ta kai shekara 14 ko 15 sai a yi mata aure. Hakan yana da kyau kamar yadda addinin ya nuna. Yin aure bai kamata ya hana ilimin mata ba amma. Abin takaicin sai a bar su a gida ba su san yadda ake tsarki ba.
Daga baya da ilimin boko ya fara shigowa kasashen Hausa, sai aka dauki karatun Boko a matsayin wani abu marar amfani. Ba a ba ’ya’ya maza da mata damar su yi karatun ba. Bayan an fara gane muhimmancin karatun boko ne, aka fara ba maza damar yin karatun sosai.
A manyan makarantun boko akwai sashi daban-daban, wadanda dalibi zai iya yin karatu. Akwai kamar Likitanci da karatun zama Injiniya da na harsuna irinsu Turanci da sauransu. A bangaren karatun likitanci da Unguwarzoma, wadannan sashi ne da mata za su fi mayar da hankali, domin hakan zai amfani al’umma. A wasu asibitocin, maza ne wadanda ba muharramai ba ke duba mata. To a maimakon haka, zai fi kyau a ce mace ta duba ’yar uwarta.
Mafi yawancin tsokacin mutane a kan karatun ’ya’ya mata a kan yanayin makarantun ne. Yadda ake hada maza da mata, yadda tsarin sanya tufafi yake da sauransu. Idan har gwamnati na so ta habaka ilimin mata a Najeriya, musamman a arewa, ya zama dole ta yi la’akari da halayya da addini da zamantakewa da kuma al’adun mutane wajen tsara makarantu da kuma yadda ake karatun, haka zai taimaka wajen bunkasa ilimi sosai a Arewacin Najeriya.
Ina so mata su sani neman ilimi wajibi ne, sai dai su sani ya zama dole su tsare kansu daga aikata dukkan ayyuka marasa kyawu, iyaye su sanya idanu wajen lura da yadda ’ya’yansu mata suke karatu.

Abubuwa 4 da ke iya zama cikas ga ilimin 'ya mace a Arewacin
Najeriya
Ga abubuwan 4 wanda sune nake ganin
zasu iya zama cikas ga ilimin ‘ya mace a Arewacin Najeriya:
Talauci: Game da bincike, kashi 28 cikin 100
sunyi imanin cewa talauci ne babban cikas ga ilimin diya mace a Najeriya. A Arewacin
Najeriya kuwa, ko shakka babu shine babban abunda yake kawo cikas. Talauci ne
ke sanya iyaye na aika yaransu mata talla wanda ke hanasu zuwa makaranta.
Al’ada:
A Arewacin Najeriya, al’adarmu tayi babban tasiri akanmu. Wanda ya shafi cigabanmu
da kuma wayewarmu. Duk da cewa anyi ittifakin cewa ilimantar da diya mace nada
muhimmanci ga al’umma, har ila yau akwai iyaye wadanda suke hana yaransu mata
karatu. Game da cewar wasu, ai aikin mace shine kula da gida. Duk da cewa
addinin musulunci ya wajabta neman ilimi da ilimantar da iyali da yara, wannan
kalubale bai gushe a Arewa ba. Rashin
sani a bangaren iyaye: Bincike ya nuna cewa kaso 18 cikin100 sun amince da
cewa jahilcin iyaye babban kalubale ne. kashi 25 sunyi imanin cewa idan aka
ilimantar da iyayen, zasu fahimici muhimmancin ilimantar da ‘ya mace. Wani
sakamakon rashin ilimi a bangaren iyaye shine, a tunaninsu idan ‘ya mace tayi
karatu, ba zata amfanesu da shi ba, illa mijinta da yaranta. Saboda haka, sai
su mayar da hankali wajen ilimantar da yara maza.
Saurin aure: Kashi 15 na mutane sun yi imanin cewa babban kalubalen da ke
zama cikas ga ilimin ‘ya mace shine aurar da su da akeyi da wuri. A wasu wurare
a Arewa, ana aurar da yara mata kafin su san ciwon kansu. Kana kuma ana aurar
da su ga jahilan mazaje wadanda ba zasu ilimantar da su bayan aurensu ba.
wannan sai ya haifar da zuriya jahila.
Nuna jinjinarka zuwa ga marubucin ta hanyar danna maballin like ko kuma ka bada taka gudunmuwa ta hanyar yin commenting da naka ra'ayi dan nuna gamsuwa zuwa ga marubucin. Yin hakan zai kara masa kwarin guiwa.

© Muhammad Sunusi Nalado
+2347030339117
Shafin Bahaushen Arewa

0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home