Thursday, 19 October 2017

Kungiyoyin Matasa.

Matasa! Shin ko kun san kuna da muhimmiyar rawa wadda zaku iya takawa a yankunanku?

Duba da yanda halinda ilimi yake a ciki a kasar mu musamman nan gida Arewa, yasa nayi wannan rubutu domin fadakarwa ga matasan mu da tunatar da su muhimmacin ilimi da kuma rawar da zasu iya takawa wajen karfafawa na kasa dasu dan cigaban mu.

Ilimantarwa da tarbiyya al’amura ne masu girman matsayi da daukaka kuma sune ginshikin rayuwa da suke kai mutum ga kyakkyawar rayuwa da samun cikan kamala. Hakika mutum wani halitta ne da ke bukatar tarbiyya a fagen rayuwarsa kuma sakamakon kyakkyawar tarbiyya  zai iya kai wa ga babban matsayi na tsarkakan ruhi da yalwan ilimi a rayuwarsa ta duniya. Hakika tun daga yarantar mutum har zuwa girmansa da kuma zuwa karshen rayuwarsa yana rayuwa ce a kan matakai masu bibiyar juna kuma a tsawon matakan rayuwarsa yana da damar kai wa ga mataki madaukaki, kamala da cika.

Hakika matakin kula da tarbiyyar yara lamari ne mai muhimmanci da ke bukatar sanya ido da lura, kuma dole ne a kan mahaifa ko masu kula da tarbiyyar yara su kasance masu cikakken sa- ido kan tarbiyyar yaran da lura da dabi’unsu. A fili yake cewa tarbiyya da ilimantarwa al’amura ne masu muhimmanci da daukaka a rayuwar mutum musamman daga lokacin yaranta zuwa lokacin samartaka, kuma wadannan matakai biyu na yaranta da samartaka suna kunshe da tarin matsaloli na musamman, sakamakon haka tarbiyya da ilimantarwa suna da matakai, kuma kowane mataki yana da nashi matsayi da muhimmanci na musamman.
Tarbiyya a ma’anarta ta lugga tana nufin karuwa, girma da habaka a kan tafarkin da ake bukata, ko kan tafarki mai kima. Yayin da neman ilimi hanya ce da take kai mutum ga samun tarbiyya da kyakkyawan sakamakon rayuwa. Don haka a fili yake cewa neman ilimi da samun tarbiyya sune shimfida kuma ginshikai da suke kai ga inganta rayuwar bil-Adama tare da taimaka masa wajen cimma burin rayuwarsa na kai wa ga matsayin cika da kamala da ake bukata.

Akwai kungiyoyi da dama masu zaman kansu wato 'Non Governmental Organisations' NGO a takaice wanda suke a nan gida Arewa sunyi niyyar taimakawa wajen bada kula ga harkokin karatu  musamman na yara kanana da kuma marayu marasa galihu, shin ko ka shirya taimakon alu'ummmar ka? Ta wace hanya zaka iya bada gudunmuwarka domin cigaban Arewa? Wannan sune tambayoyi wanda ya kamata kayiwa kanka su.
Wata kungiyar matasa da naci karo da su ne yasa nayi wannan 'yar tunatarwar ga matasan mu na Arewa domin ganin yanda suka shirya tsaf dan tallafawa yaran Jahar Zamfara wurin karatun su.
A kasa zaka iya ganin su a cikin hoto. Ko da gani, ba sai an gaya maka ba lallai sun shirya tsaf dan ganin cewa yaran jahar su sun samu tallafi daga garesu. Shin ko kaima kana da niyyar taimakawa dan ganin an karfafawa ilimi a Arewa?

Wannan kungiyar matasan da na hadu da su a wata makaranta mai suna Ibrahim Gusau sun yiwa kansu suna da Juvenile Aid Foundation.

Wasu daga cikin Matasa 'yan kungiyar Juvenile Aid Foundation


Hakika wadannan matasa abun koyi ga sauran matasa da suke da karfi da kuma ikon tallafawa iyakar gwargwado domin ganin ilimi ya samu shiga a cikin dukkan wani kauye da ke Arewacin kasar nan.

A kasa zaku iya ganin yara 'yan makaranta da kuma sauran matsan nan na kungiyar Juvenile Aid Foundation.

Yara ;yan makaranta.
Idan ka duba daga kasa kuma, zaka ga shugaban Kungiyar yayin da yake mika kyauta ga wani dalibi.
Sugaban Kungiya yayin da yake mika kyauta ga wani dalibi.









Labels: ,

Monday, 16 October 2017

Yadda aure ke sauya mutane a tsawon rayuwa

"Wane dalili ne yasa ake da dimbim mata masu shekaru talatin da doriya basu da aure a kwanakin nan?"



A dakin taron walima na shirin kundin Bridget Jone wanda ya yi matukar sabo da kowane rukunin mutane da suka saba haduwa da su, a kebe, kewaye da abokai masu aure a daki guda.
Duk da cewa masana aikin kwakwalwa ba su samu cikakkiyar fahimtar da za ta tabbatar da cewa ko aure na sanya wa mutane natsuwa da gamsuwa.
Kamar kawayen Bridget ko kuma ana ingiza mutane ne kawai su ji suna son yin aure.
Bincike ya nuna cewa wadanda suka jajirce wajen haduwa don zaman rayuwa da wani mutum hakika suna samun sauyi da kimar mutuntaka a yanayin jin dadi da wahala.. har mai rabawa ta raba mu.
Al'amarin na da ma'ana baya ga cewa, nuna haduwar zaman tare da wani mutum a bainar jama'a na nuni da biyayya da hangen gaba.
Ba ma a yi la'akari daukacin sauyin tsarin rayuwa ga wasu, tabbas zaman tare na yau da kullum da mutum guda na matukar bukatar hakuri da masalahar zaman lumana.

Hattara ma'auratan da suka gamsu da juna: duk da cewa ana samun jin dadi na takaitacen lokaci ne, domin bayan an daura aure, cikin shekara guda sabani na iya sanyawa a sake lale.
Dangane da kowane irin sauyin kyautata rayuwa aure ke da tasirin haifarwa, abin tunani da alamar tambaya a kai shi bincike ya bai wa fifiko a daukacin fadin duniya, tun da miliyoyinmu na daura aure a kowace shekara.
A gaskiya, binciken da aka gudanar kan tambayar mamakinta ba shi da kima.
Ta yiwu mafi kyawun hujja ita ce wacce ta bayyana a nazarin baya-bayan nan da aka gudanar a kasar Jamus, inda masu binciken suka bi kadin sauyin mutuntakar al'umma kusan 15,000 a tsawon shekaru hudu.
An gano cewa marasa aure irin Bridget Jones da suka jajirce kan lamarin sun fi farin ciki.
Muhimmmin al'amari dai shi ne mutum 664 da aka bibiyi harkokinsu sun yi aure ne lokacin da suke karatu.
Inda aka kyale Jule Specht a Jami'ar Münster da abokan aikinta suka gano yadda kimar mutuntakarsu (halayyarsu) ta sauya in an kwatanta da sauran wadanda ba su da aure da aka bibiyi kadin lamarinsu.

Masu binciken sun gano cewa masu auren da aka yi binciken kansu an samu raguwar baza harkokin rayuwarsu a bainar jama'a in an kwatanta da sauran.
Bambancin da aka samu matsakaici ne, amma duk da haka ta yi wu ya bayar da hujja ingantacciya kan zargin da gwagware ke yi cewa abokansu masu aure ba sa shakatawa da holewa kamar yadda suke yi.
Duk da abin mamakin da a ke bazawa, ma'aurat ba kasafai suke suke daukar dabi'un (ha;layar) junansu a tsawon lokaci ba.
Tsarin nazarin ya tabbata ne musamman a kan mata, kamar yaddda yake kunshe a wani kwarya-kwaryar bincikee da aka gudanar a Amurka aka wallafa shi a shekarar 2000.
Inda masu binciken suka yi gwaji kan halayyar mutane fiye da 2000 masu matsakaitan shekaru da aka bibiyesu sau biyu tsawon shekaru shida zuwa tara.
A wancan lokacin, mata 20 masu aure, yayin da wasu 29 aka sake su.
Idan an yi kwatanceceniya tsakanin masu aure da wadanda aurensu ya rabu, wadanda suka samu rabuwar aure sun fi sakin jikinsu a bainar jama'a, kamar wadanda aka cire musu sasarin igiyar aure.
Sababbin ma'aurata maza kuwa, alamu na nuna sun yi matukar fa'idantuwa in an kwatanta da takwarorinsu wadanda suka samu rabuwar aure, inda suke nuna matukar halin kula da kwazo, sannan damuwarsu ta yi matukar raguwa.
Halin kula da ke bai wa maza masu aure kwarin gwiwa haka kawai yake bijirowa.
Duk mutumin da ke da aure (ko tarayyar masoya ta tsawon lokaci) zai san cewa akwai dimbin basirar da ake amfani da ita don tabbatar da dorewar auratayya wajen tarairayar harkokin gida masu tangal-tangal da jirrgin ruwan masu aure.
Wadannan su ne hakikanin al'amuran da aka gano sabuwar makalar da ka wallafa cikin wannan shekarar.

Maza masu aure sun fi nuna halin kula, kodayake a wasu lokutan sukan bar tufafinsu da suka yi dauda warwatse a daben daki.
Tawagar Jamusawan yamma masana aikin kwakwalwa, karkashin jagorancin Tila Pronk na Jami'ar Tilbug sun tabbatar da cewa mafi muhimmancin dabarar zamantakewar aure ko halayya shi ne iya tarairayar kai (yin dauriya da cijewa ta tsawon lokaci saboda aure) da yafiya.
Wato ta yadda za aka iya share abin da ya gabata na daga kuskure aboki/abokiyar zama a wani yanayi, wato kamar watsi da kayan sawa a kasa ko yabawa da nuna sha'awa makwafta.
Masu binciken sun dauki sababbin ma'aurata 199, inda suka auna kimar tasirin yafiya ga juna cikin watanni uku da aurensu wadanda aka bi Kadin lamarinsu an kiomanta amincewarsu da abubuwa kamar haka:
"Idan abokin zamana ya yi mini ba daidai ba, masalauha kawai in yafe kuma in manta" da yadda suke tarairayar kansu (wadanda aka bi kadin lamarinsu an kimanta aminceewarsu da al'amura kamar "Na iya kauce wa yaudarar daukar hankali").
Wadanda aka bibiyi lamarinsu an sake maimaita gwaje-gwajen a kansu kowace shekara har tsawon shekaru hudu.
Sakamakon binciken ya yi nuni da cewa wadanda aka bibiyi al'amauransu sun kara kaimin yafiya da tarairayar kansu tsawon lokacin da aka gudnar danazarin.
Kididdigar alkaluma ta nuna karuwar yafiya ta kasance tsaka-tsaki, yayin da karin iya tarairayar kai (kamun kai) ya zama kadan, amma Pronk da abokan aikinta sun yi nuni da cewa karuwar daidai take da ta kame kai da aka gano a mutanen da ke tsarin tunani musamman kokarin da aka yi wajen kama kai.
Masa aikin kwakwalwa ba su warware abin da ake son ganowa kan ko mutane na samun gamsuwar rayuwa da daina shan wuya idan sun yi aure.
Mene ne dalilin da ya sanya ma'aurata ke watsar da gamsuwar jin dadin rayuwa?
Muhimmiyar hujja ta bayyana a wasu nazarce-nazarce da aka gudanar kan gamsuwar rayuwa da sauye-sauyen samun farin ciki bayan aure.
Rukunin marasa aure irrin su Bridget Jones masu shekaru 30 da doriya za su yi murnar jin cewa duk da gamsuwar dadin rayuwa na karuwa bayan aure, aka kuma samu dalilin da zai haifar da koma-baya a sake lale bayan shekara guda.
Sai dai a iya cewa daukacin abin da aka gano ba lallai haka yake akan kowa ba.
Mun sha yin batu kan wasu mutane da ake kimanta su a matsayin miji nagari ko mata tagari (yayin da wasu sun fi son kasancewa a rayuwar gwagwarci), wannan mahangar madogara ce, domin hujja ta yi nuni kan yadda ma'aurata ke samun sauyin rayuwar farin ciki ya bambanta bisa la'akari da kimar mutunta ko halayyarsu kafin aure.
A wajen wasu, aure na samar da madawwamin farin ciki: musamman abin da ya shafi kula da kai da kunyar mata da sakin jikin maza da ke nuni da karin annashuwa da gamsuwar rayuwa in an yi aure, karara yake a bayyane saboda sababbin ma'aurata na da tsarin rayuwa da ya yi daidai da kimar mutuntakarsu (irin halayensu), duk da cewa dai har yanzu ba a yi nazarin al'amarin ba.

Mutanen da ke da aure ba su cika sakin jikinsu ko kai tsaye su yi ganganci aikata wani abu ba.
Karshen al'amuran, ko me za a ce kan abin da aka baza cewa ma'aurata kan dauki halayen junasu tsawon lokaci?
Akwai tabbaci kan haka in an yi la'akari da yadda tsofaffin ma'aurata ke sanya riga 'yar shara ko kayan motsa jiki szuna masu barkwanci.
Ta yiwu lamarin na da rikitarwar ban mamaki.
Idan haka kuwa, ana sa ran ma'auratan da suka dade da juna halayyarsu za ta yi daidai da ta abokan zamansu.
Sai dai masu bincike daga Jami'ar Jihar Michigan sun yi nazarin tantance halayyar ma'aurata fiye da 1,200, inda suka gano cewa alakar kadan ce ko ma babu ita sam kan wannan lamari.
Hakikanin gaskiya ita ce mutane da halayyarsu ta zamo iri guda sun fi auren juna karon farko.
Idan aka dauki al'amuran dungurrungum, binciken na nuni da cewa yana da matukar wuya a ce aure na sauya dabi'a.
Sai dai lamarin ba shi da alaka rudani da rikicin dan Adam da ka biyo baya, inda haihuwa 'ya'ya ke zuwa akai-akai.



Labels:

Sakon maraba daga marubucin shafin Bahaushen Arewa.



Assalamu Alaikum 'yan uwa Hausawa.
Wannan shine karo na farko da nake son fara tura sakonnina zuwa gareku domin nuna kauna da kuma kyautata alaka ta tsakanina da ku a matsayina na Bahaushe mazaunin Arewa.

Na zauna nayi nazarin ganin wace hanya zan bi domin bada tawa gudunmuwa a wannan zamani da muke ciki, bayan 'yan shawarwari da na samu da kuma bincike-bincike da suka gudana, sai na yanke shawarar bude wannan shafi na Bahaushe.

Wannan shafi nawa na Bahaushen Arewa zai mayar da hankali ne a kan labaru wanda suka kunshi namu na gida, ina nufin na Arewa da kuma ma wanda suka shafi kasar mu Nigeria baki daya. Sannan kuma wannan shafi zai mayar da hankalinsa ne ga siyasar mu ta arewa da kuma ta kasa baki daya duba ga yanda matasan Arewa suka fara mayar da hankalin su kan siyasa.
Zan dinga kawo maku labaru da dumi-dumin su ku karanta a cikin nutsuwa ba tare da ka jira wani ya baka labari ba, sai kuma dan nazari da bincike da nayi wanda ya shafi matasan mu domin kawo muna cigaba. Sannan shafin zai dinga watsa manufofinsa ne ta yaren harshen Hausa kamar yanda kuke gani a sakon maraba da kuke karantawa yanzu.

Ina mika gaisuwata ga dukkan wani Bahaushe da yake zaune a gida Arewa ko a waje. Ina fata wannan manufa tawa ta kasance hanyar hada kyakyawar alaka ta a tsakanina da ku.
Sannan daga karshe ina mai fata Allah Ubangiji ya bani sa'a domin gudanar da harkoki na cikin sauki da kuma nasara, Allah ya kare ni daga aikata barna.

Allah ya kawo muna saukin rayuwar da muka tsinci kan mu a wannan kasa tamu ta haihuwa. Allah ya yaye muna dukkanin bakin ciki da kuma asara a duniya da kiyama.