Tuesday, 7 November 2017

KO KUN SAN MUHIMMANCIN MATA KUWA?



ILIMI DA MUHIMMANCINSA GA MATA
Kafin zuwan wayewar kai da ilimi, mata basu da fada  aji cikin al’umma. An dauki mata ba a bakin komi ba face masu dawainiyar gida da kula da ‘yara. A zamanin jahiliyyah a kasar Saudiya birne ‘ya’ya mata akeyi da ransu, mata basu da gado, an dauke su kamar rigar da ake canzawa ko wane lokaci aka ga dama.
Karatun ‘ya mace ba karamar fa’ida yake da shi al’umma ba. Sabili da mahaifiya ita ke tare da yara kullum a gida, ilimin zai sa kanta ya waye ta san muhimmancin karatu, zuwa asibiti, bawa yaranta tarbiyyah ta kwarai ta inda har zasu zama masu kishin kasa. Mace me ilimi zata taimaka wurin bawa mijinta shawarwari masu amfani da zasu taimaka wurin gudanar da harkokin yau da kullum.
Har ila yau, yara mata dake karkara ana tauye musu hakkin su na rashin samun ingantaccen ilimi ta hanyar aurar dasu tun a shekarun da basu wuce kirgen dangi ba. Wala Allah in tasami miji me kishin karatu yasakata, wala Allah kuma ta qare da jinyar yoyon fitsari bayan mijin ya mata sakin wulakanci.  Ba addinin da ya hana neman ilimi a duniya. Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace  neman ilimi wajibi ne akan kowane Musulmi, Tirmidhi ne ya ruwaito shi lamba ta saba’in da hudu.
Shawarar da zan bawa gwamnati shine, a saka dokar dole sai yarinya ta kai shekaru sha shida kafin a aurar da ita. Akalla kafin nan ta kara sanin ciwon kanta, ta gama karamin mataki na  makarantar gaba da firamari da kuma ilimin yin ginshiqan musulunci ba tare da ta kwafsa ba. A kuma saka taran duk mahaifi koh marikin yarinyar da ya aurar da ita kafin shekarun da aka kayyade  koh ya hana ta zuwa makaranta ya biya kudi masu yawan gaske koh zaman gidan maza na shekaru adadin kudin.
A lokutan baya, ba a  baiwa ilimi muhimmanci ba kuma ba a damu a ba ‘ya mace ilimin addini ba ballantana na zamani. Har ana cewa “Sabbi saukar Mata”. Watau da sun kai Suratul Sabbi shi ke nan sun bar karatu da neman ilimi. Suratul Sabbi kuwa ita ce Surah ta 97 a Alkur ‘ani, kuma ita ce Izifi na daya daga cikin Izifi Shittin na Alkur’ani.

Mace a wancan zamanin, idan ta kai shekara 14 ko 15 sai a yi mata aure. Hakan yana da kyau kamar yadda addinin ya nuna. Yin aure bai kamata ya hana ilimin mata ba amma. Abin takaicin sai a bar su a gida ba su san yadda ake tsarki ba.
Daga baya da ilimin boko ya fara shigowa kasashen Hausa, sai aka dauki karatun Boko a matsayin wani abu marar amfani. Ba a ba ’ya’ya maza da mata damar su yi karatun ba. Bayan an fara gane muhimmancin karatun boko ne, aka fara ba maza damar yin karatun sosai.
A manyan makarantun boko akwai sashi daban-daban, wadanda dalibi zai iya yin karatu. Akwai kamar Likitanci da karatun zama Injiniya da na harsuna irinsu Turanci da sauransu. A bangaren karatun likitanci da Unguwarzoma, wadannan sashi ne da mata za su fi mayar da hankali, domin hakan zai amfani al’umma. A wasu asibitocin, maza ne wadanda ba muharramai ba ke duba mata. To a maimakon haka, zai fi kyau a ce mace ta duba ’yar uwarta.
Mafi yawancin tsokacin mutane a kan karatun ’ya’ya mata a kan yanayin makarantun ne. Yadda ake hada maza da mata, yadda tsarin sanya tufafi yake da sauransu. Idan har gwamnati na so ta habaka ilimin mata a Najeriya, musamman a arewa, ya zama dole ta yi la’akari da halayya da addini da zamantakewa da kuma al’adun mutane wajen tsara makarantu da kuma yadda ake karatun, haka zai taimaka wajen bunkasa ilimi sosai a Arewacin Najeriya.
Ina so mata su sani neman ilimi wajibi ne, sai dai su sani ya zama dole su tsare kansu daga aikata dukkan ayyuka marasa kyawu, iyaye su sanya idanu wajen lura da yadda ’ya’yansu mata suke karatu.


Abubuwa 4 da ke iya zama cikas ga ilimin 'ya mace a Arewacin Najeriya
Ga abubuwan 4 wanda sune nake ganin zasu iya zama cikas ga ilimin ‘ya mace a Arewacin Najeriya:

 Talauci: Game da bincike, kashi 28 cikin 100 sunyi imanin cewa talauci ne babban cikas ga ilimin diya mace a Najeriya. A Arewacin Najeriya kuwa, ko shakka babu shine babban abunda yake kawo cikas. Talauci ne ke sanya iyaye na aika yaransu mata talla wanda ke hanasu zuwa makaranta.
Al’ada: A Arewacin Najeriya, al’adarmu tayi babban tasiri akanmu. Wanda ya shafi cigabanmu da kuma wayewarmu. Duk da cewa anyi ittifakin cewa ilimantar da diya mace nada muhimmanci ga al’umma, har ila yau akwai iyaye wadanda suke hana yaransu mata karatu. Game da cewar wasu, ai aikin mace shine kula da gida. Duk da cewa addinin musulunci ya wajabta neman ilimi da ilimantar da iyali da yara, wannan kalubale bai gushe a Arewa ba. Rashin sani a bangaren iyaye: Bincike ya nuna cewa kaso 18 cikin100 sun amince da cewa jahilcin iyaye babban kalubale ne. kashi 25 sunyi imanin cewa idan aka ilimantar da iyayen, zasu fahimici muhimmancin ilimantar da ‘ya mace. Wani sakamakon rashin ilimi a bangaren iyaye shine, a tunaninsu idan ‘ya mace tayi karatu, ba zata amfanesu da shi ba, illa mijinta da yaranta. Saboda haka, sai su mayar da hankali wajen ilimantar da yara maza.
Saurin aure: Kashi 15 na mutane sun yi imanin cewa babban kalubalen da ke zama cikas ga ilimin ‘ya mace shine aurar da su da akeyi da wuri. A wasu wurare a Arewa, ana aurar da yara mata kafin su san ciwon kansu. Kana kuma ana aurar da su ga jahilan mazaje wadanda ba zasu ilimantar da su bayan aurensu ba. wannan sai ya haifar da zuriya jahila.

Nuna jinjinarka zuwa ga marubucin ta hanyar danna maballin like ko kuma ka bada taka gudunmuwa ta hanyar yin commenting da naka ra'ayi dan nuna gamsuwa zuwa ga marubucin. Yin hakan zai kara masa kwarin guiwa.


© Muhammad Sunusi Nalado
+2347030339117
Shafin Bahaushen Arewa


Labels: ,

Wayar Salula:Zuma ga Zaki ga Harbi




A wannan zamani da muke, idan ka duba a cikin al’ummar mu, waya ta zama ruwan dare a tsakanin kananan yara da matsan mu, ganin haka ne ma yasa marubucin yayi nazari game da irin illar da waya take yi ga matasa da kananan yara.
Ita Kalmar karamin yaro a kundin tsari tana nufin yaro ko yarinya wanda bai haura shekaru 18 ba (a takaice wanda bai balaga ba) dalili kuwa shine a bincike na masana sun yi amanna da cewa sai mutum ya kai shekara 18 ne ya soma mallakar hankalinsa, a wannan shekaru ne dokar kasa ta hau kan shi.
To a hakikanin gaskiya, duk abu wanda aka kirkira, yanada alfanu, haka zalika yana da illoli tari duk da cewa shi Alexander Graham Bell (wanda ya kirkiri wayar tarho) bai da makusa, yayi amfani da hikimarsa ne wurin bada tasa gudunmuwa dan cigaban dan Adam a rayuwa duk da cewa an samu wasu sauye-sauye bayan tashi fasahar. Ban sani ba ko akwai wata doka da ta hana matasa ‘yan kasa shekara da 18 amfani da wayar salula ba, saboda har yanzu akan bincike nake dan gani ko zan samu. Kididdiga ta nuna cewar kaso 78% a cikin 100% na yara dake tsakanin shekara 12-17 sun riga sun mallaki wayar salula. Amfani da wayar salula da matasa ‘yan kasa da shekara 18 ke yi ya zama barazana ba ma akan su kawai ba, a’a har ma ga al’umma duka.
A nan marubucin ya iyakance kansa ga illolin wayar salula a hannun matasa da kananan. Kafin mu tattauna illolin, ga wasu daga cikin amfaninta/muhaimancinta:
    

  •   Zumunci: Waya ta taimaka sosai wurin sada zumunci. Sada zumunci ta hanyar hada ‘yanuwa wanda suke nesa da juna.
  • Kasuwanci: Waya tana taimakawa wurin gudanar da harkokin kasuwanci. Manyan ‘yan kasuwa da ma kanana suna amfani da waya sosai domin gudanar da harkokin kasuwancin su, a yau mai son siyan kaya a wurin wani dan kasuwa zai iya daga wayarsa daga gida ya kira abokan cinikin sa dan siya ko siyar da hajarsa a nan  gida Najeriya ko a kasar waje.
  • Agajin gaugawa: Wayar salula ta taka muhimmiyar rawa wurin sadarda agaji na gaugawa. Misalin maras lafiya zai iya amfani da wayarsa dan kiran wani dan’uwan nasa ko kuma ya kira likita domin dauki a gareshi.
To wannan kadan kenan daga cikin alfanu na wayar salula, wanda zai iya kasancewa manya har matasan suna amfanuwa da shi. Amma illolin wayar salula gasu zan zayyano a kasa; 

Lalacewar tarbiyya: Saboda samun cigaba na zamani da ya auku, kamar yadda aka ambata a baya, wayar salula tayi jagora sosai da gaske wurin wargaza tarbiyyar matasa. Idan kayi duba ga yanar gizo gizo, akwai manhjoji da suke basu da aiki wanda ya wuce zuba hotuna da bidio na kallo wanda suke kunshe da batsa da nuna tsiraici. A bincike na masana da aka gudanar kwana-kwanan nan ya nuna cewar akwai irin wadannan manhajoji akan yanar gizo sama da dubu dari. Haka binciken ya nuna cewa, Najeriya tana daya daga cikin kasashe wanda sukafi kowa shiga wannan shafuffuka, wannan abun iyaye su duba ne, su saka ido akan ‘yan ‘yansu domin ganin sun kubutar da su daga irin shafuffukan, dalili kuwa shine kowa ya sani a addinnace walau Krista ko Musulmi cewa bayyanar da tsiraici bai karbuwa ga al’ummar mu domin yana taimakawa wurin rugejewar tarbiyya da samun barna ta bangaren fyade, haka ma yana ruguza al’umma da imaninsu. Akwai abunda ake kira da ‘cybersex’ a turance, ma’anarsa shine zina ta yanar gizo ko shafukan sada zumunta wanda hakan yana faruwa ba tare da sanin iyaye ba. Yana faruwa ta hanyar kiran waya ko kuma zance a shafukan sada zumunta. Masu wannan dabi’a suna bin hanyar taba al’aurar su dan su biyawa kansu bukata. Wannan ba karamin fasadi bane garesu da kuma al’umma baki daya.

Haduwa da abokai bata gari: A nan Kalmar aboki bata gari yana nufin aboki wanda yake neman wanda zasu yi tarayya da shi wurin wata harka ta barna. Daga gida ko a wani wuri, wani saurayi zai iya hada lambobi a wayarsa ya danna kira, burinsa ya samu mace ta daga wayar. Idan yayi nasa kuwa ya samu macen ta dauka sai ya gabatar da manufofinsa, idan itama ra’ayinta yayi daidai da nasa shikenan sai barna ta auku. Idan kuwa yayi rashin nasara aka samu akasin bata karbi ra’ayin nasa ba, sai yayi kokarin jawo hankalinta da kalamai har ta dawo ta amince da zancensa saboda karancin wayo.
    
     Tabarbarewar Karatu: Binciken masan ya nuna cewar yawan amfani da da wayar salula da matasa keyi yana haifar da koma baya ga iliminsu. Wannan ne ma yasa makarantu da dama suka hana dalibansu mu’amula da wayar salula yayinda suke cikin farfajiyar makaranta. Daliln haka kuwa abune mai saukin fahimta. A wannan zamani da muke ciki ya sanya bincike yayi karanci a tsakanin matasanmu ta hanyar yin amfani da shafin ‘Matambayi Baka Bata’ wato GOOGLE turance. Yana taimakawa wurin satar amsa matuka. Shi wannan shafin yasa matasanmu sun manta amfanin dakunan karatu wato ‘Library’. Sannan kuma ita wannan salular tana kunshe da na’urar lissafi da na’urar daukar hoto, duka wannan suna taimakawa wurin dauke hankali a lokacin darasi.
    
     Cãca: Shafuka da ake ta kirkirowa a yanzu dangin cãca sun zama ruwan dare. Misalin irin su akwai ‘9jabet, NairaBet, 365bet’ sun taimaka kwarai wurin afkawar matasanmu da yara kanana cikin halaka domin shafin yana bada dama da duk wanda ya shiga yayi zabi tsakanin kungiyoyin kwallon kafa wadda za tayi nasara akan wata ta hanyar sadaukar da wasu kudade.
  
     Rashin Isasshen Barci: Hakika barci yana da matukar amfani ga matashi. A kowacce rana matashi yana bukatar yayi barci na awa 9 da rabi to amma wasu basu amfani da wannan damar dan ganin sun cimma wanna awowin suna barcin sai dai su mayar da hankalinsu ga yanar gizo ko shafukan sada zumunta irin su Facebook ko Whatsapp. Zaka ga matashi ya kwashe lokaci mai tsawo yana rike da wayarsa, ya hana idanunsa runtsawa  a karshe sai kaga yaro idan yaje aji wurin darasi ka sameshi yana barci wannan illar ta jawo koma baya ta hanyar neman ilimi.

        Sirri: A wannan zamani da muke ciki yanzu, zamani ne wanda sirrin mu gaba daya bamu da tabbacin sa kuma yana kara kasancewa cikin barazan idan muka barshi a fili ta hanyar da makiya zasu iya amfani da shi wurin zambatarmu da wannan damar. Abun mamaki ne ga yanda wani bincike ya nuna cewar kashi 52 na matasa basu kashe na’urar GPS da ke a cikin salularsu idan suna amfani da yanar gizo ko shafukan sada zumunta. Wasu har sun kai matsayin da suna yada adireshin su a shafukan sada zumunta, daukar hotuna a gidajen su suna aikawa kai har ma hada lokaci na sirri dan saduwa ta fuska da wani wanda basu taba gani ba a zahiri sai dai fira a yanar gizo. Wannan bai tsaya nan ba, wasu sun kai matsayin suna bayyana zuri’arsu ko rayuwarsu wadda ta shafesu ga abokai da ko wani bako a shafukan sada zumunta.  Ni da kaina nayi badda kama nayi fira da wata karamar yarinya, abubuwanda ta fada mun game da rayuwarta ya gigita ni, har ta kai tana fada mun sirrikanta na boye. Wannan abu ne mai matukar tsoratarwa.


Iyaye sun bijiro da dalilai daban-daban  da yasa suke so ‘ya’yansu su mallaki wayar salula. Ya kamata ayi nazari mai zurfin gaske tsakanin amfaninta da kuma illolinta kafin a basu damar rika wannan na’ura. Wani mai bincike ya saki bidiyo na kallo inda ya nuna yanda yake magana da matasa a asirce ta shafukan sada zumunta kai har ma hada wata haduwa ta musamman a wani kebantaccen wuri. Yayi hakan ne tare da sanin iyayen su  dan ya nusar da su iyayen illar wayar salula. Zaka iya kaddara yanda karshen labarin ya kasance idan ace wani mutum ne wanda ba’a san asalin sa.

Balaga, kaifin tunani da kalar wayar dake hannun matasa da makamantansu, sune ya kamata a duba kafin a baiwa wani matashi damar rike waya. Haka zalika, tsauraran matakai na bukatuwa wurin kula da hanyoyi da yara suke mu’amula da waya. 
Kar ka manta ka danna maballin like dan nuna jijinawarka ga marubucin. Bugu da kari ma, zaka iya bata taka gudunmuwa ta hanyar yin comment dan nuna jin dadinka. Yin hakan zai kara kwarin guiwa ga marubucin.
© Muhammad Sunusi Nalado
+2347030339117
Sahfin Bahaushen Arewa
2017.

Labels: ,